Labarai
Zaben 2027: Dattawan APC a Jigawa Sun Bayyana Goyon Baya ga Tinubu da Umar Namadi
Daga Usman Muhammad Zaria
Kwamitin Dattawan jam’iyar APC a Jihar Jigawa ya amince da Bola Ahmed Tinubu da Umar Namadi a matsayin ’yan takarar jam’iyar a zaɓen 2027.
An cimma wannan matsaya ne a wani taro da ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga matakai daban-daban.
Shugaban APC na jihar, Ahmed Garba MK, ya ce an ɗauki matakin ne bayan dogon nazari.

Ya bayyana cewa sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, yayin da aka amince da Namadi a matsayin ɗan takarar gwamna.
Ya ƙara da cewa kwamitin dattawa zai ɗauki nauyin sayen fom ɗin takara ga dukkansu.
Jam’iyyar ta kuma zaɓi tsarin sulhu maimakon zaɓen fidda gwani domin zaɓar ’yan takara.

Domin aiwatar da wannan tsari, an amince da kafa kwamitoci a matakin jiha da ƙananan hukumomi.
Kwamitocin za su tabbatar da tantance duk masu neman takara kafin fitar da ɗan takara guda daya a kowanne muƙami.
Hakazalika wakilan yankunan majalisar dattawa uku sun bayyana cikakken goyon bayansu ga wannan matsaya.

Dattawan jam’iyyar sun bayyana amincewar a matsayin wadda aka yi gaba ɗaya ba tare da wani sabani ba.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
