Connect with us

Labarai

Yan Sandan Bauchi Sun Kama Wani Kan Satar Yaro Da Kisan Kai

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da aikata garkuwa da yaro da kuma kisan kai, a wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a cikin birnin Bauchi. Lamarin ya fito fili ne bayan da wani mazaunin unguwar Nasarawa Madina, Salisu Yunusa, ya kai rahoto ga ‘yan sanda cewa dansa mai shekaru hudu, Yunusa Salisu, ya bace tun ranar 18 ga watan Maris da safe.

Mai magana da yawon rundunar SP Nafiu Habibu ya bayyana cewar mahaifin yaron, bayan bacewar dansa sai ya samu kira daga wata lambar waya da ba a sani ba a ranar 19 ga watan Maris, inda aka bukaci ya biya kudin fansa na naira dubu dari biyar domin a sako yaron. Duk da cewa ya biya naira dubu dari guda domin ceto dansa, amma bai sake ganin yaron ba, lamarin da ya kara tayar masa da hankali tare da sanya shi garzayawa ga jami’an tsaro.

Bayan samun rahoton, jami’an bincike na ofishin ‘yan sanda na ‘C’ Division karkashin jagorancin DPO suka fara gudanar da bincike cikin gaggawa, wanda ya kai ga cafke wani matashi mai suna Rabiu Safiyanu mai shekaru 20, wanda yake zaune a unguwar daya da iyalan yaron. Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin yana da kusanci da iyalan yaron, kasancewarsa abokin kanin mahaifin yaron kuma yana da damar shiga gidan ba tare da wata shakka ba.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin cewa shi ne ya dauki yaron, inda daga bisani ya shake shi har ya mutu, sannan ya kai gawarsa wani wuri da ake kira Warinje Hills ya jefar. Har ila yau, ya amsa cewa shi ne ya kira mahaifin yaron domin neman karin kudin fansa duk da cewa ya riga ya kashe yaron.

Jami’an ‘yan sanda sun samu nasarar gano gawar yaron a wurin da aka jefar da ita, inda aka tarar da alamun shakewa a jikinsa, tare da igiya da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin. Likitan ‘yan sanda ya tabbatar da mutuwar yaron, sannan aka dauki hotunan gawar kafin a mika ta ga iyalansa domin yi masa jana’iza a wurin bisa dalilan lafiyar jama’a.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin mika shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin zurfafa bincike tare da tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu cikin gaggawa. Haka kuma ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu lura da mutanen da ke kewaye da su tare da kai rahoton duk wani abu da ya zama abin zargi ga jami’an tsaro.

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara