Labarai
Kwastam ta Kama Kayayyaki na Sama da Naira Miliyan 478 a Jihar Kwara
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Hukumar Kwastam ta Kasa reshen Jihar Kwara ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta shigowa da su ko kuma aka takaita, da kudinsu ya haura Naira miliyan 478 a bana.
Mukaddashin shugaban hukumar a yankin Jihar Kwara, Mataimakin Kwanturola Najeem Ogundeyi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai kan ayyukan hukumar a jihae .
Ya ce hukumar ta kuma samar wa gwamnati kudaden shiga da suka kai sama da Naira biliyan 2 da miliyan 500, wanda hakan ke nuna irin gudunmawar da take bayarwa wajen tallafawa manufofin tattalin arzikin gwamnati.

A cewarsa, hukumar na da kudurin kare tattalin arzikin kasa tare da tabbatar da bin doka da oda.
Ogundeyi ya kara da cewa hukumar za ta tabbatar da cewa jihar ba ta zama mafakar masu safarar haramtattun kayayyaki ba, yana mai gargadin cewa duk wanda ya yi yunkurin tauye tattalin arzikin kasa ta hanyar fasa kwauri zai fuskanci hukunci mai tsauri.
Ya bayyana cewa duk da gargadi da ake yi akai-akai, har yanzu ana ci gaba da safarar kaya ta barauniyar hanya, musamman shigo da shinkafa daga kasashen waje ba bisa ka’ida ba, lamarin da ke barazana ga manoman gida da kuma samar da abinci a kasa.

Ogundeyi ya ce haramta shigo da irin wannan shinkafa wata muhimmiyar dabara ce ta karfafa gwiwar manoma na cikin gida, samar da ayyukan yi, da kuma wadata kasa da abinci.
Ya kara jaddada cewa wadannan nasarorin da aka samu sun samo asali ne daga sahihan bayanan sirri da kuma hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankunan kan iyaka, ‘yan kasuwa da daukacin jama’a da su hada kai da hukumar domin kare masana’antun cikin gida, kiyaye tattalin arzikin kasa, da kuma bunkasa ci gaba mai dorewa.

Daga cikin kayayyakin da rundunar ta kama sun hada da motoci guda biyar, buhuna 1,107 na shinkafar waje, buhuna 44 na sukari da aka shigo da su daga kasashen waje, jarkoki 317 na man fetur (PMS), buhuna 120 na ma’adinin lithium da aka hako ba bisa ka’ida ba, da kuma daruruwan kayan sawa wato gwanjo, da kayayyakin gyaran motoci.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
