Labarai
Azumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dakta Builder Muhammad Uba, ya kaddamar da rabon tallafin kudi domin taimaka wa marasa galihu a yankin yayin watan Ramadan mai alfarma.
Da yake jawabi a lokacin rabon tallafin, Dakta Muhammad Uba ya bayyana cewa an zabo wadanda suka amfana daga dukkanin kananan hukumomi 11 na Birnin Kudu.

Ya kara da cewa, jimillar mutane 110 sun karbi naira 20,000 kowannensu, yayin da wasu mutane 50 kuma suka karbi naira 50,000 kowannensu, domin rage radadin halin da iyalai da daidaikun mutane ke ciki a wannan wata na Ramadan.
A cewarsa, shirin na da nufin rage wa al’umma radadin matsin tattalin arziki a lokacin Ramadan.

Ya kuma bukaci wadanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kudaden yadda ya dace.
Dakta Muhammad Uba ya nuna godiya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na tabbatar da jin dadin al’ummar jihar.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun bayyana godiyarsu ga shugaban karamar hukumar, inda suka ce wannan tallafi ya zo a kan lokaci.
Sun kuma yi addu’ar fatan alheri da samun nasara ga shugaban karamar hukumar da kuma Gwamna Umar Namadi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
