Labarai
Gwamnatin Kwara Ta Miƙa Kayan Aiki Ga Asibitin Harabar KWASU Osi
Gwamnatin Jihar Kwara ta miƙa kayan aikin asibiti da na jinya ga asibitin harabar Osi a jami’ar Jihar Kwara a wani ɓangare na ƙudirin ta na ci gaba da samar da ingantattun kuma sauƙaƙa samun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.
Yayin gabatar da kayan, Babbar Sakatariyar Hukumar Bunƙasa Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Jihar Kwara, Farfesa Nusirat Elelu, ta jaddada aniyar gwamnati na gina Kwara mai koshin lafiya ta hanyar zuba jari mai ɗorewa a fannin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da kuma haɓaka ma’aikata.
Ta yabawa gwamnan jihar bisa jagoranci nagari da kuma ƙoƙarinsa na tabbatar da adalci da daidaito wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a dukkanin ƙananan hukumomi 16 na jihar.
Farfesa Elelu ta bayyana cewa sauye-sauye da tsare-tsare da shirin gyare-gyaren da gwamnati mai ci ta aiwatar a fannin lafiya sun fara haifar da sakamako mai auna, kamar yadda aka gani a ƙididdigar lafiyar ƙasa baki ɗaya.
A cewarta, jihar ta lashe gasar Jagorancin Kiwon Lafiya a Matakin Farko har sau uku a jere, ta kuma zama ta farko a Yankin Arewa ta Tsakiya wajen shirin ko-ta-kwana a fannin lafiya. Haka kuma, an san jihar a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka fi dacewa a haihuwa a Nijeriya, sakamakon raguwar mace-macen mata masu juna biyu da na jarirai.
“Waɗannan nasarori ba kwatsam aka same su ba; sun samo asali ne daga tsare-tsare masu ma’ana, horaswa da sake horas da ma’aikatan lafiya, ingantacciyar kulawa da kuma ɗaukar sabbin ma’aikata domin ƙara ƙarfi wajen ba al’umma kulawa mai inganci,” in ji ta.
A nata jawabin bayan karɓar kayan a madadin jami’ar, Shugabar Harabar Osi kuma Dekanar Tsangayar Kimiyyar Muhalli, Farfesa Binta Suleiman, ta nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa gaggawar amsa bukatar da jami’ar ta gabatar.
Ta bayyana tallafin a matsayin mai muhimmanci kuma da ya zo a kan lokaci, tana mai cewa amincewa da gaggawar kawo kayan aikin asibitin na nuna damuwar gwamnati ta gaskiya kan lafiyar ɗalibai da ma’aikata.
Kayan aikin da aka miƙa sun haɗa da gadon asibiti da katifu, na’urorin gwajin jini (centrifuge), kujerun ɗakin jira, bututun gwaje-gwajen dakin gwaje-gwaje, na’urorin auna hawan jini (sphygmomanometer), kayan aikin jinya, auduga, takalman asibiti, zanen gado, matasai da sauran muhimman kayan kiwon lafiya.
ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
