Ilimi
Majalisar Matan Shugabannin Afirka Ta Karrama Oluremi Tinubu Kan Ayyukan Tallafa wa Mata da Yara
Daga Bello Wakili
Majalisar Matan Shugabannin Kasashen Afirka OAFLAD ta karrama Uwargidan Shugaban Ƙasar Nijeriya, Oluremi Tinubu sakamakon gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ilimin ‘ya’ya mata.
Karramawar ta kuma yaba da shirye-shiryen da ta aiwatar domin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, tare da faɗaɗa tallafin jin ƙai ga iyaye mata da yara a faɗin Nijeriya.
Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa Nana Shettima ce ta wakilci Oluremi Tinubu a babban taron Majalisar ta OAFLAD karo na 29 da na 30 da aka gudanar a Addis Ababa na ƙasar Ethiopia.
OAFLAD, wadda ke aiki ƙarƙashin shirin ta na “We Are Equal”, wato ‘Duk Daya Kuke’, na ci gaba da fafutukar tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, ƙarfafa tattalin arzikin mata, da inganta samun ilimi a faɗin nahiyar Afirka.
Majalisar ta kuma jaddada buƙatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka domin magance matsalolin da ke addabar mata da yara, musamman a yankunan da rikice-rikice suka shafa.
A jawabinsu wajen taron, Uwargidan Shugaban Ƙasar Sierra Leone kuma Shugabar OAFLAD, Fatima Maada Bio, tare da Uwargidan Shugaban Ƙasar Ghana, Lordina Mahama, sun yaba wa Sanata Oluremi Tinubu bisa yadda take ci gaba da fafutukar kare haƙƙin mata da yara tare da aiwatar da shirye-shirye masu amfani a Nijeriya da ma wajenta.
Dakta Bio ta jaddada alaƙar da ke tsakanin ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya, inda ta ce ba za a iya tabbatar da cikakken haƙƙin mata ba a wuraren da ke fama da rashin tsaro da rikice-rikice.
Haka kuma, Misis Mahama ta nuna muhimmancin ci gaba da tallafawa ilimin ‘ya’ya mata da kuma ƙarfafa mata masu sana’o’i, a matsayin hanyar gina rayuwa mai ɗorewa.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
