Connect with us

Labarai

Kwastam da Gwamnatin Kebbi Sun Kulla Haɗin Gwiwa kan Hanyar Safarar Kaya ta Nijar–Benin yayin da Gwamnatin Tarayya ta Buɗe Hanyoyin Kasuwanci

Published

on

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta kulla haɗin gwiwa ta musamman da Gwamnatin Jihar Kebbi domin aiwatar da hanyar wucewar kaya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ita, wadda za ta bai wa kayayyakin da ke tafiya zuwa Jamhuriyar Nijar damar wucewa ta cikin Jamhuriyar Benin.

Da yake jawabi yayin karɓar Shugaban Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Bashir Adewale-Adeniyi, a ziyarar ban girma da ya kai jihar Kebbi, Gwamna Nasir Idris ya tabbatar da cewa jihar ta shirya tsaf domin yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya don tabbatar da gudanar da ayyukan wannan hanya cikin sauƙi da inganci.

Gwamnan ya yaba da salon jagorancin Shugaban Kwastam, Adewale-Adeniyi, tare da nuna godiya ga tawagar Jamhuriyar Benin bisa haɗin kai da suka bayar.

Tun da farko, Shugaban Kwastam ya bayyana cewa wannan shiri zai magance cikas da ake fuskanta a harkar wucewar kaya, ya kare tsaron ƙasa, tare da tabbatar da cewa ana kammala fitar da kaya cikin awanni 48 ta hanyar amfani da sabbin fasahohi domin hana karkatar da kaya zuwa inda ba a nufa ba.

Ya yi gargaɗi cewa ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki da suka karya dokokin wucewar kaya za su fuskanci hukunci mai tsanani, yana mai jaddada cewa rashin bin ƙa’ida na iya haifar da shingayen kasuwanci ba na haraji ba tare da raunana amincewa tsakanin ƙasashe maƙwabta.

Shugaban Kwastam, wanda Gwamna Idris da tsofaffin gwamnoni biyu suka tarbe shi cikin girmamawa duk da sanar da ziyarar sa’o’i 24 kacal, ya yaba da ruhin ’yan’uwa da haɗin kai na al’ummar Jihar Kebbi, tare da nuna muhimmancin jihar a tsarin tsaron Nijeriya.

Ya ƙara da cewa kayayyakin da ke fitowa daga tashar jiragen ruwa ta Apapa da filayen jiragen sama na Nijeriya zuwa ƙasashen makwabta za a tantance su kuma a motsa su cikin awanni 48, ba tare da tauye tsaron ƙasa ko muradun tattalin arziƙi ba.

COV: SANI DUTSINMA

Labarai

Labarai15 hours ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai19 hours ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai2 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai3 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai3 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Labarai3 days ago

Arewa Za Ta Saka Wa Tinubu Da Ruwan Kuri’a A 2027- Yari

Daga Usman Muhammad Zaria  Daraktan Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce...

Labarai3 days ago

Shettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bukaci ’yan Najeriya da su goyi bayan sake zaɓen Shugaba...

Labarai4 days ago

Jigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz

Daga Usman Muhammad Zaria Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan harkokin yada labarai da wayar dan...

Labarai4 days ago

Majalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027

Daga Khadijah Aliyu  Majalisar Dokokin Jihar Kano na shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2027 daga Gwamna Abba Kabir Yusuf...

Mafi Shahara