Labarai
Gwamnatin Zamfara Ta Fara Biyan Bashin Garatuti Kashi na Biyu
Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da fara biyan bashin garatuti da ake bi wa tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, wanda ya shafi zangon daga Janairu 2024 zuwa Satumba 2025.
Wannan mataki ya biyo bayan umarnin Babban Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin ƙarfafa walwalar ma’aikatan gwamnati da kuma dawo da amincewar jama’a ga shugabanci.
An bayyana wannan amincewa ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Muhammad Dantawasa, ya fitar, inda ya bayyana cewa wannan biyan bashin shi ne kashi na biyu na biyan garatuti, kuma ana sa ran fara sakin kuɗaɗen cikin ’yan kwanaki masu zuwa.
A cewar sanarwar, an tsara wannan shiri ne domin rage nauyin matsin tattalin arziƙi da tsofaffin ma’aikata ke fama da shi na tsawon lokaci, tare da sake jaddada ƙudirin gwamnati na cika alƙawura ga waɗanda suka yi wa jihar hidima da gaskiya.
Kwamishinan ya ƙara da cewa biyan bashin garatuti muhimmin ginshiƙi ne na Ajandar “Rescue Mission” ta Gwamna Lawal, wadda ta bai wa walwalar ma’aikata, tsare-tsaren kuɗi masu inganci da kuma adalcin zamantakewa muhimmanci.
Gwamnan ya kuma jaddada cewa tsofaffin ma’aikata sun cancanci mutunci, girmamawa, da biyan hakkokinsu a kan lokaci.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ba a buƙatar wani mai cin gajiyar shirin ya nema ko ya roƙi wata alfarma daga kowane mutum ko ofishi domin karɓar kuɗinsa. Duk tsofaffin ma’aikatan da aka tantance kuma suka cancanta za a biya su yadda ya kamata ba tare da nuna wariya ba.
Yayin da take yabawa da haƙuri da fahimtar tsofaffin ma’aikata, gwamnati ta tabbatar da cewa za a ci gaba da biyan sauran kashi-kashi gwargwadon wadatar kuɗi, tare da sake jaddada ƙudirin ta na cika dukkan manufofin Ajandar “Rescue Mission” domin amfanin al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya.
REL/AMINU DALHATU
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
