Labarai
An Shawarci Ɗalibai su Ɗauki Ilimin kula Laburare a Matsayin Sana’a
A wani gagarumin goyon baya ga wani fanni na ilimi da ba a cika ba shi muhimmanci yadda ya kamata Shugaban Jami’ar North West University Sokoto, Farfesa Muktar Umar Bunza, ya shawarci ɗalibai da su yi la’akari da Ilimin dakunan karatu Laburare da Kimiyyar Bayanai (Library and Information Science – LIS) a matsayin sana’a mai matuƙar muhimmanci kuma mai amfani.
Ya bayar da wannan shawara ne yayin da yake karɓar baƙuncin wata tawaga daga Hukumar Rijistar Laburare ta Najeriya a babban harabar jami’ar da ke Jihar Sokoto.
Farfesa Bunza ya bayyana fannin Ilimin Laburare da Bayanai a matsayin ginshiƙi mai matuƙar muhimmanci a wannan zamani, yana mai jaddada cewa a zamanin da ake cike da bayanai amma ana fama da ƙarancin sahihin ilimi, ma’aikacin laburare da masanin bayanai su ne jagororin da ke tsara, sarrafa, da fahimtar bayanai yadda ya dace.
Ya ƙara da cewa wannan fanni ba wai kawai ajiye littattafai ba ne, illa dai shi ne tushen tattalin arzikin ilimi, ginshiƙin bincike na kimiyya, kuma ƙofar samar da ’yan ƙasa masu ilimi da fahimta.
Farfesan ya kuma yi bayani kan yadda fannin ke ci gaba da sauyawa, inda ya nuna yadda yake haɗuwa da fasahar zamani ta dijital, sarrafa bayanai, adana tarihi da takardu, da kuma tsaron bayanai ta yanar gizo (cybersecurity).
Ya bayyana cewa, sakamakon ƙarancin ƙwararrun masana Ilimin Laburare da Bayanai a ƙasar nan, waɗanda suka kammala karatu a wannan fanni kan samu aiki cikin sauƙi.
A baya, jagoran tawagar ziyarar kuma Rijistar Hukumar, Jakada Jafaru Abdullahi Wase, ya ce sun ziyarci jami’ar ne domin gudanar da binciken tantancewa da bin ƙa’idoji na yau da kullum, wanda ya shafi duba matsayin shirin LIS, kayan aikinsa, manhajar karatu, da bin ƙa’idojin ƙwararru na ƙasa.
Jagoran tawagar ya yaba da jajircewar jami’ar wajen inganta fannin, yana mai jaddada cewa zurfin fahimta da goyon bayan da Mataimakin Shugaban Jami’ar ke bai wa wannan sana’a abin a yaba ne ƙwarai.
Nasir Malali
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
