Labarai
Gwamna Bago Ya Yi Alkawarin Kammala Duk Ayyukan da Ake Gudanarwa a Jihar Neja
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya sake tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar kammala dukkan ayyukan hanyoyi da ake aiwatarwa a fadin jihar.
Gwamnan ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake duba wasu manyan ayyukan hanyoyi a garin Bida.
Daga cikin ayyukan hanyoyin da Gwamna Umar Bago ya duba sun haɗa datagwayen hanyar Minna zuwa Bida, tsohon aikin gada na Titin legacy da kuma gadar da ke haɗa hanyar Minna zuwa Abuja. Haka nan ya duba aikin hanyar zagaye mai tsawon kilomita 44 ring road da kuma gadar musayar hanya interchange bridge da ke Western Bypass na Bida.
An bayyana cewa idan aka kammala aikin ring road, zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa, musamman na manyan motoci masu ɗaukar kaya, da ke haddasa cunkoso a cikin garin Bida, tare da rage gurbatar muhalli da hatsarurrukan hanya. Gwamnan ya kuma duba tagwayen hanya mai tsawon kilomita 11, daga Bida Low Cost zuwa haɗuwa da Bida Western Bypass, wadda ta kai kashi 70 cikin 100 na kammala aiki.
Gwamna Umar Bago ya kuma duba hanyar da ke kaiwa fadar Mai Martaba Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Neja.
Dukkan wadannan manyan ayyukan hanyoyi da Gwamna Umar Bago ya fara aiwatarwa na daga cikin sabbin tsare-tsaren sake gina jihar Neja, ƙarƙashin Ajandar Sabuwar Neja, da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar.
PR / Aliyu Lawal
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
