Kasuwanci
’Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyukan Katsina, Sun Kashe Mutane 8
’Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka huɗu a Ƙaramar Hukumar Dandume ta Jihar Katsina, inda suka kashe mutane takwas tare da jikkata wasu mutum goma sha ɗaya da raunuka mabambanta.
Maharan, waɗanda suka kai harin a ƙauyukan Baraje, Kirijan, Shugu, Kauran Pawa da Unguwar Jika da tsakar dare, sun kuma yi garkuwa da mutum guda tare da lalata gidaje da wuraren kasuwanci.
Yayin da ba a samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar domin tabbatar da faruwar lamarin ba, majiyoyi da dama daga al’ummomin da abin ya shafa sun tabbatar wa Rediyon Najeriya aukuwar harin.
Wani mazaunin Baraje, Malam Nura, ya shaida wa Rediyon Najeriya ta wayar tarho cewa maharan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare, inda suke haska fitilu tare da harba bindiga ba kakkautawa cikin gidajen mutane.
Ya bayyana cewa an riga an binne gawarwakin waɗanda suka rasu, yayin da ake ci gaba da ba wa waɗanda suka jikkata kulawar lafiya a Babban Asibitin Funtua.
Mazauna yankin sun nuna takaicinsu kan harin, inda suka ce hakan ya saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya da aka cim ma a bara tsakanin ’yan bindiga da al’ummomin yankin, wadda kowanne ɓangare ya ɗauki alƙawarin ɗaukar matakan da za su ƙarfafa zaman lafiya.
Isma’il Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
