Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Shekarar 2026

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2026 na Naira biliyan 901 da miliyan 804, domin inganta ci gaban jihar tare da biyan buƙatun al’ummar Jigawa.

Da yake jawabi bayan sanya hannu kan kasafin, Gwamna Namadi ya bayyana cewa duk da kasafin jihar ya kai sama da Naira Biliyan, kasafin kuɗin haɗin gwiwa na ƙananan hukumomi 27 ya kai Naira Biliyan 288 da Miliyan 805.

Wannan kasafi sakamakon shirin tattaunawa da al’umma ne da muka gudanar, kuma yana nuna ainihin muradu da burin mutanen Jihar Jigawa.

Saboda haka, kasafin al’umma ne, daidai yadda jama’a suka buƙata, kuma daidai abin da ke ƙunshe a cikin wannan kasafi,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya kuma yabawa mambobin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa bisa jajircewa da sadaukarwar da suka nuna a duk tsawon aikin kasafin kuɗin.

Goyon bayansu a yayin tarukan tattaunawa da al’umma, ganawar bangarori biyu, tattaunawa ta manyan shugabanni, da kuma matakan kwamitoci, ya taka muhimmiyar rawa wajen amincewa da wannan kasafi cikin nasara,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma yabawa mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar bisa amincewa da kuma shiga  shirin tattaunawa da al’umma, tare tattara ra’ayoyin jama’a, inda da dama daga cikinsu ke aiki har cikin dare.

Haka nan, Namadi ya yaba wa al’ummar jihar bisa goyon baya da kuma halartar su a tsarin kasafin kuɗin, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi iya ƙoƙarinta wajen inganta rayuwar al’ummar Jigawa.

 

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara