Ilimi
Jigawa Za Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 6 Don Bunkasa Noma, Ilimi Da Kasuwanci
Majalisar Zartarwar Jihar Jigawa ta amince da wasu manyan kwangiloli da kudinsu ya haura Naira Biliyan 6, domin karfafa bangarorin noma, ilimi da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna kudirin gwamnatin jihar wajen inganta muhimman bangarori da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.
A cewarsa, majalisar ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2 domin sayen babura nau’in Hunter guda 1,180 ga malaman gona a fadin jihar.
Ya ce wannan mataki ya yi daidai da kokarin Gwamna Umar Namadi na bunkasa harkar noma da raya karkara. Baburan za su taimaka wajen saukaka zirga-zirgar malaman gonan domin su rika koyar da manoma sabbin hanyoyin noma da za su taimaka wajen samun karin amfanin gona.
Haka kuma, majalisar ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2 da miliyan 300 domin gina sabbin kasuwanni na zamani a Maigatari, Shuwarin da Hadejia.
Kwamishinan ya bayyana cewa, wannan shiri na da nufin karfafa hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida da samar da yanayi mai kyau don kasuwanci da ciniki.
Alhaji Sagir ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da Naira Biliyan 1 domin gina katanga a makarantun gwamnati 15 a fadin jihar, domin kare rayuka da dukiyoyin dalibai da malamai tare da inganta yanayin karatu.
Bugu da kari, majalisar ta amince da kwangilar sama da Naira Biliyan 1 da miliyan 300 domin sayen injinan nika shinkafa na zamani guda 200, da kayan aikin walda, da na kera kayayyaki da kayan yin fenti, don cibiyar koyon sana’o’i ta zamani da aka kammala ginawa a Limawa, karamar hukumar Dutse.
Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen hanzarta kokarin gwamnatin jihar na samar da ayyukan yi ga matasa marasa aikin yi da kuma karfafa sana’o’in dogaro da kai.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
