Kasuwanci
Obasanjo Ya Kaddamar da Cibiyar Taro Ta Duniya Ta Ahmadu Bello A Bauchi.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed.
Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba.
Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan wurare na inganta hadin kai da bunkasar tattalin arziki, inda ya kara da cewa dole ne Najeriya ta ci gaba da sanya kanta a matsayin mai shiga tsakani a harkokin duniya.
Gwamna Bala Mohammed ya nuna jin dadinsa ga goyon bayan Obasanjo, inda ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan da za su bunkasa ilimi, yawon bude ido, da ci gaban tattalin arziki a fadin jihar.
Sannan ya bayyana cewa Cibiyar Taro ta kasa da kasa ta Ahmadu Bello ta tsaya a matsayin shaida kan manufofin gwamnatinsa na mayar da Bauchi cibiyar tattaunawa, kirkire-kirkire, da zuba jari a Arewacin Najeriya.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, cibiyar za ta kasance cibiyar hada-hadar kudi ta gida da waje, da suka hada da taron ilimi, taron kasuwanci, da nune-nunen al’adu.
Cov/Alhassan
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
