Labarai
Za a Yi Aikin Hadin Gwiwa Tsakan KNUPDA Da NSCDC A Kano
Hukumar Tsare-tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) ta jaddada aniyar ta na karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da inganta ci gaban birane ta hanyar hadin gwiwa da hukumar tsaro ta NSCDC.
Tawaga daga KNUPDA, karkashin jagorancin Manajan Darakta, Arc. Hauwa Hassan T/Wada, ta kai ziyarar gani da ido hedikwatar hukumar NSCDC da ke Kano a wani bangare na kokarin fahimtar juna da hadin gwiwa tsakanin hukumomi.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Arc. Hauwa ta bayyana cewa ingantaccen tsare-tsare da ci gaban birane na bukatar hada karfi da karfe da manyan jami’an tsaro domin tabbatar da kare kadarorin gwamnati, tabbatar da doka da oda a cikin babban birni.
Ta bayyana irin shirye-shiryen KNUPDA da ke ci gaba da bita da aiwatar da tsare-tsare da nufin inganta tsarin birane, da magance haramtattun gine-gine, da kuma inganta kyawun birnin Kano.
Ta kuma bayyana cewa yin aiki da hukumar NSCDC zai kara karfafa bin doka da oda da kuma taimakawa wajen kare ayyukan ci gaba a fadin jihar.
A nasa martani, kwamandan hukumar NSCDC na jihar Kano, Mista B. B. Bodinga, ya bayyana jin dadinsa da ziyarar tare da yabawa KNUPDA bisa kokarin da take yi na samar da hadin kai tsakanin hukumomin.
Ya kuma ba da tabbacin hukumar ta NSCDC a shirye ta ke na bayar da tallafin tsaro da ya dace da kuma yin aiki tare da KNUPDA domin cimma burin gwamnatin jihar na samar da ci gaban birane cikin tsari da dorewa.
Taron ya kuma gabatar da wani zaman tattaunawa inda bangarorin biyu suka tattauna batutuwan da suka dace da juna, da suka hada da kare kadarorin jama’a, aiwatar da ka’idojin tsare-tsare, da dabarun inganta tsaro da bin ka’ida a birane.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
