Labarai
Gwamnan Kwara Ya Yabawa Shugaba Tinubu
Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara.
Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin.
Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun.
Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Ta ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya gana da Shugaba Bola Tinubu a ziyarar da ya kai a Jos.
Ta yabawa shugaban kasa bisa wannan goyon baya, da kuma babban hafsan soji da jami’an tsaro na hadin gwiwa bisa sabon matakin kawar da duk wata barazana ga lafiyar jama’a a jihar.
A kwanakin baya ne hedkwatar rundunar ta umarci babban hafsan sojin kasa na GOC 2 Manjo Janar CR Nnebeife da ya koma Kwara domin gudanar da ayyukan dawo da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma yabawa ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, babban hafsan soji, babban hafsan soji na 2, da duk wani jami’in tsaro.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
