Ilimi
Yara Kusan Miliyan 3 Za A Yiwa Rigakafin Cutukan Polio Da Kyanda A Jihar Sakkwato
An yi wa yara miliyan biyu da dubu takwas allura, yayin aikin rigakafin cutar Polio, kyanda, da kuma Gaida a jihar Sakkwato.
Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin da aka gudanar a garin Bodinga da ke karamar hukumar Bodinga.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Garba Muhammed, Alhaji Ahmed Aliyu ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa aikin polio din zai gudana ne a daukacin unguwanni 244 dake fadin jihar.
Don haka ya yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da kuma abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki da su ba da himma wajen tallafa wa wannan aikin ta hanyar hada kai da kuma tabbatar da cewa duk yaran da suka cancanta sun samu alluran rigakafin da ake bukata.
A cewar sa, za a yi allurar rigakafin ga yara ‘yan watanni 9 zuwa 14, kuma za a kwashe kwanaki 10 ana yin wannan aikin.
Ya bayyana cewa Najeriya ce tafi kowacce kasa yawan yara masu kamuwa da cutar kyanda da gaida a duniya.
Ya kara da cewa lamarin ya nuna akwai gagarumin gibi a fannin rigakafi na yaran da ba sa karbar alluran rigakafin a daidai lokacin da ya kamata, wanda ke haifar da munanan sakamako kamar kuramta, makanta, da sauran matsaloli.
Gwamnan wanda mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idris Mohammed Gobir ya wakilta, ya jaddada aniyar gwamnatinsa na gina tsarin kiwon lafiya wanda ba wai kawai ake iya samunsa ba, har ma da samar da ingantacciyar kulawa da tallafawa gano cututtuka da wuri.
A nasa jawabin kwamishinan lafiya na jihar Dr. Faruk Umar Abubakar Wurno ya bayyana cewa an samar da rukunin ma’aikata da zasu ziyarci unguwanni 244, inda kowane rukunin ma’aikatan akwai mutum 11 a cikin su.
Dakta Faruk Umar Wurno ya kara da cewa, jihar ta samu alluran rigakafi guda 3,072,520 daga hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa.
Kwamishinan ya kuma yi amfani da damar wajen mika godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa bada tallafin da takwarorinta ke yi na wannan aikin.
Da yake tsokaci, wakilin mai alfarma Sarkin Musulmi kuma Hakimin Wurno, Alhaji Kabir Alhassan Cigari, ya bayar da tabbacin cewa sarakunan sun jajirce wajen ganin an cimma nasarar shirin.
MUSTAPHA/Sakkwato
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
