Kasuwanci
Shugaba Tinubu Ya Bada Umurnin A Rage Kudin Aikin Hajjin Bana
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci hukumar jin daɗin alhazai ta Najeriya NAHCON da ta rage kuɗin Hajjin bana, inda ya buƙaci hukumar ta fito da sabon kuɗin nan da kwana biyu.
Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ne ya bayyana wannan buƙatar a ganawarsa da shugabannin hukumar a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja a ranar Litinin.
Ya yi kira da a samu ƙarin haɗin kai tsakanin hukumar a matakin ƙasa da takwarorintna na jihohi ciki har da gwamnoni domin a samu sauƙin gudanar da aikin Hajjin na bana.
Da yake ganawa da manema labarai bayan taron, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hadejia ya ce an yi taron ne domin ƙarƙare shirye-shiryen Hajjin na bana, ciki har da tattaunawa game da kuɗin kujera.
“Saboda yadda farashin naira ya haɓaka da kuma sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnatin Najeiya da aka fara gani, shi ne mataimakin shugaban ƙasa ya ce yana ganin idan har maniyyata sun biya tsakanin naira miliyan 8.5 zuwa miliyan 8.6 a bara, yanzu da darajar naira ta ɗaga, ya kamata a ga canjin da aka samu a kuɗin Hajjin bana.”
A nasa ɓangare, sakataren hukumar alhazan, Dr Mustapha Mohammad ya ce wannan matakin zai taimaka wajen ƙara yawan mahajjatan bana.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
