Kasuwanci
Kungiyar Miyetti Allah Ta Musanta Zargin Boye Makamai A Cikin Garken Shanu
Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) reshen jihar Kwara ta yi watsi da zargin cewa mambobinta na boye makamai a cikin shanunsu domin gujewa jami’an tsaro.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar, Alhaji Shehu Garba ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a Ilorin.
Ya ce Hausa Fulani da Bororo a jihar su ne masu bin doka da oda kuma ba su da wani laifi a kan haka.
Shugaban na MACBAN ya yi zargin cewa mayar da tsohon Sarkin Fulanin Igangan da ke Oyo, Alhaji Saliu Abdulkadir zuwa jihar Kwara a shekarar 2021, da kuma sauran makiyayan da suka yi tashe-tashen hankula ne suka haddasa matsalar tsaro a jihar.
Alhaji Garba ya bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su sanya ido kan ayyukan tsohon Sarkin Fulanin Igangan da sauran masu ci-rani don hana kwatankwacin abin da ya faru a Oyo a Kwara.
Shugaban kungiyar ta MACBAN ya tabbatar wa gwamnatin jihar kan kudirinsu na bayar da gudunmuwar domin rage matsalolin tsaro a jihar zuwa mafi karanci.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
