Kasuwanci
Sashen Dauko Rahotanni Na NUJ Ya Sami Sabbin Shugabbanni A Nasarawa
Mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Nasarawa sun zabi sabbin jami’anta da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon shekaru uku masu zuwa.
Shugaban kwamitin zaben, Mista Samson Osuo, ya sanar da Abubakar Abdullahi na jaridar Daily Trust a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 21 da Danjuma Joseph na National Accord da kuri’u 9 a matsayin shugaban kungiyar.
Ya kuma bayyana cewa Mista Chris Nyamtu na gidan rediyon Najeriya ne ya yi nasara da kuri’u 21 yayin da Augustine Kuza na jaridar Pilot na Najeriya ya samu kuri’u 9 a matsayin Sakatare.
Mista Abel Daniel na jaridar Guardian a matsayin mataimakin shugaba
Awayi Kuje na NAN a matsayin Mataimakin Sakatare, Michael David na Daily Independent a matsayin Sakataren Kudi.
Wasu kuma. Collins Agwam na jaridar Punch a matsayin Ma’aji da Aliyu Muraki na Rediyon Najeriya Kaduna a matsayin mai bincike.
Ya kuma yabawa ’yan kungiyar bisa yadda suka kammala zaben sannan Shugaban NUJ na Jihar Nasarawa, Salihu Alkali, ya yaba wa shugaban kungiyar da ya da wa’adinsa ya kare, Mista Isaac Ukpoju bisa yadda aka samar da hadin kai, zaman lafiya da kuma tabbatar da zaman lafiya
Ya kuma bukaci ’yan uwa su ci gaba da bin ka’idojin sana’arsu, yana mai cewa ba zai amince da duk wani aiki na rarraba kan jama’a ba.
Aliyu Muraki/Lafia.
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
