Kasuwanci
Shugaban Colombia zai kori jakadun Isra’ila daga ƙasar
Shugaban Colombia Gustavo Petro ya ce zai kori dukkanin jami’an diflomasiyar Isra’ila daga ƙasarsa a matsayin martani ga kama jiragen ruwa masu ɗauke da agaji zuwa Gaza.
Ya kuma ya bayyana cewa an yi garkuwa da yan Colombia guda biyu.
Petro babban mai caccakar yaƙin Isra’ila a Gaza, ya zargi Isra’ila da sake saɓa dokokin ƙasa da kasa inda ya buƙaci sakin su cikin gaggawa.
Italiya ta kira kutsen jiragen ruwan da Isra’ila ta yi a matsayin fashin teku da kuma ta’addanci.
An dai yi ƙokarin shigar da kayan agaji ne ta hanyar teku domin kaucewa shingen Isra’ila a yankin
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
