Kasuwanci
Akwai Bukatar Daukar Matakan Gaggawa Don Maganin Tsaro A Jahohin Arewa
Kungiyoyin Kare Muradun Arewa, wato Arewa Defence League, sun fitar da sanarwar da suka kira October Declaration, wadda ta tanadi matakai na gaggawa don magance matsalolin tsaro, koma bayan tattalin arziki da kalubalen rayuwa a Arewacin Najeriya.
Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar, ya bayyana hakan a taron dabarun da aka gudanar a Arewa House Kaduna, inda ya ce “lokacin alkawura marasa amfani ya wuce, wannan sanarwa kuwa ita ce alkawarinmu ga mutanen Arewa.”
Ya yi gargadi kan karuwar ta’addanci da ‘yan bindiga, rashin aikin yi da kuma yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, lamarin da ya danganta da gazawar shugabanci da kuma rashin wakilci nagari.
A cewarsa, kungiyar ba ta da manufar ballewa daga kasa, amma akwai gaggawar bukatar sabuwar yarjejeniya tsakanin shugabanni da jama’a domin dawo da amincewa da adalci.
Shugaban ADL ya kuma sanar da shirye-shiryen gudanar da babban Taron ‘Yan Arewa, samar da cikakkun manufofin ci gaba, tare da kaddamar da kamfen din wayar da kan masu kada kuri’a kafin zaben 2027.
Shettima A.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
