Labarai
Manchester United Na Zawarcin Kane, Mainoo Na Son Ya Bar Old Trafford
Manchester United na zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 32, wanda zai iya barin Bayern Munich a bazara mai zuwa.(Star), external
Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce Kane, wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din, ‘za su karbe shi da hannu biyu” idan ya dawo , amma ba ya tsammanin dan wasan zai bar kungiyarsa ta Jamus a yanzu.(Sky Sports), external
Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, ya soma shirin barin Manchester United a watan Janairu domin neman wata kungiyar kwallon kafa .Ya samu wata kungiya da ta nemi a ba ta shi aro sai dai Man U ta yi watsi da tayin a bazara . (Mirror), external
Bayern Munich na tunanin sabunta kwantiragin dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 23, bayan an alakanta shi da komawa Liverpool.(Liverpool Echo), external
Arsenal ta tuntubi dan wasan Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, amma Juventus, wacce ta ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi masa a lokacin bazara, ta kimanta shi kan Yuro miliyan 80 zuwa 100 . (Tutto Juve via Goal, external)
Chelsea na sha’awar dan wasan bayan Faransa Ismael Doukoure, mai shekara 22, wanda a halin yanzu yana kungiyar Strasbourg mallakar BlueCo, a dai dai lokacin da wasu kungiyoyin firimiya da dama ke zawarcinsa.(TBR Football), external
Aston Villa na son dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho mai shekara 25 ya cigaba da taka mata leda na din din, Man U ce ta bada aron dan wasan ga Aston Villa. (National World)
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
