Connect with us

Ilimi

Ba Rabo Da Gwani Ba Shekaru 35 A Radio Nijeriya Kaduna

Published

on

Daga Ibrahim Idris Kaurar Namoda
A Ranar 20 ga Watan Satumban 1990 Habibu Tabari ya fara aiki da Radio Nigeria Kaduna, Shekaru 35 kenan da Suka gabata, inda ya fara aiki a matsayin karamin Ma’aikaci a Sashen Shiirye Shirye.

Habibu Tabari ya gabatar da Shirye Shirye da suka hada da gabatar da Zabe da Filin ‘Yan Club,, da wasa Kwakwalwa da shirye shirye addinin musulunci kamar rabin sa’ar Makarantar Sheikh Abubakar Gummi.

Shirye shirye Hajjin Bana da Tafsiran Alkur’ani Mai Girma da dai sauran shirye shirye. Sai dai shirin da Habibu Tabari yayi fice a Radio Nigeria Kaduna shi ne Jakar Magori da a shekarun baya.

 

Ya yi suna a matsayin Dan Autan Jakar Magori. Kasantuwarshi  karami a shekaru cikin masu kawo rahotanni a shirin wanda daga bisani ya zamo Madugu kuma Jagoran shirin har lokacin da ya zamo mai kula da shirin Jakar Magori dama sauran shirye shirye.

 

Habibu Tabari ya halarci kwasa kwasai a Kwalejin horas da Ma’aikatan Radio Nigeria dake Ikeja a birnin Ikko dama kwasa kwassai da dama.

 

Habibu Tabari kwararren ma’aikacin Radio ne da ya koyar da na kasa dashi dama koyar da da yawan masu neman sanin makamar aiki dama masu yiwa kasa hidima.

 

Sanin aikin Radio da kwarewar Habibu Tabari ya sa a ranar 30 ga watan Ogostan wannan shekara ta 2025 Kungiyar Ma’aikatan Radio da Talabiji da Masu wasan kwaikwayo reshen Radio Nigeria Kaduna ta karrama Habibu Tabari a matsayin Gwarzon shekara wajen Shirye- Shirye baya ga wasu karramawar da ya samu a shekarun baya.

 

A wannan rana ta 20 ga watan Satumban 2025 Habibu Tabari ya cika shekaru 35 a matsayin ma’aikacin Radio Nigeria Kaduna ranar da aikin shi ya zo karshe.

 

Sashen Sirye Shirye dama Radio Nigeria Kaduna hada da masu sauraren Radio Nigeria Kaduna za su yi kewar Muryar Habibu Tabari, sai dai Ilmin da ya bari za a ci gaba da amfana dashi duk da akan ce Ba Rabo da Gwani ba Maida Kamarshi.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara