Labarai
Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Kaduna Ranar Juma’a
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci jihar Kaduna ranar Juma’a 19 ga watan Satumban 2025.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaba Tinubu zai halarci daurin auren Nasirudeen Yari, ɗa ga Sanata Abdul’aziz Yari, da ke wakiltar Zamfara ta Yamma, da Amaryarsa Shehu Idris.
A yayin wannan ziyara, shugaba Tinubu zai kuma ziyarci Hajia Aisha, matar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidansu da ke Kaduna.
Ana sa ran shugaban zai koma Abuja a ranar, nan take bayan kammala ziyarar.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
