Connect with us

Ilimi

Birtaniya Ta Ware Fam Miliyan 19  Domin Karfafa Gina Makarantu da Cibiyoyin Lafiya A Kano

Published

on

Gwamnatin Birtaniya, ta hannun ofishin kula da kasashen renon Ingila (FCDO) tare da haɗin gwiwar UNICEF, ta ware Fam Miliyan 19  domin ƙarfafa gina makarantu da cibiyoyin lafiya masu jure sauyin yanayi a Najeriya.

A ƙarƙashin shirin samar da abubuwan dake jure yanayi na fari (CRIBS), Jihar Kano ta amfana da gyaran makarantu da asibitoci guda 55.

Wannan tallafi ya haɗa da sabunta makarantu 28 da cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda 27, cikin haɗin gwiwa da gwamnatin Jihar Kano.

Yayin bikin ƙaddamar da makarantar firamare ta Wangara a ƙaramar hukumar Gezawa, wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana cewa gyare-gyaren sun haɗa da hanyoyin zamani masu dacewa da sauyin yanayi, irin su ginin da ke da ƙarfin jure ambaliya, da kuma amfani da hasken rana don samar da wutar lantarki.

Ta kuma bayyana cewa gyaran zai ba mata damar haihuwa cikin aminci, tabbatar da samun magani cikin lokaci ga yara, da kuma bai wa matasa damar ci gaba da karatu ba tare da katsewa ba.

Daraktar ofishin jakadancin Birtaniya a Abuja, Cynthia Rowe, wacce babbar mai ba da shawara kan ilimi na FCDO, Joseph Wales ya wakilta, ta bayyana cewa shirin CRIBS ya tabbata ne ta hanyar haɗin gwiwa da UNICEF, da Gwamnatin Tarayya, da  Bankin Duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Sextant Foundation, JigSaw, Fab Inc, Crown Agents.

Shirin CRIBS na nuni da yadda gine-ginen da ke jure sauyin yanayi za su iya inganta samun kulawa ga al’ummomi masu rauni. Muna fatan wannan tsari zai ƙara samun amfani a faɗin Najeriya,” in ji ta.

Haka kuma, UNICEF tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kano, Gwamnatin Kanada, da IHS Towers Nigeria, sun ƙaddamar da na’urar samar da iskar numfashi ta oxygen a asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari  da ke Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.

Tun da farko, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda kwamishinan ilimi Dr Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya bayyana wannan aikin a matsayin  sauyi mai alfanu ga rayuwar al’umma.

Ya jaddada cewa ƙaddamar da makarantar firamare ta Wangara da kuma kaddamar da na’urar samar da iskar oxygen ta farko da ke amfani da hasken rana a jihar, sun zama ginshiƙi wajen samar da iskar da za ta ceci rayuka, musamman na yara da mata masu juna biyu.

Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin jihar wajen karewa da kula da wadannan wurare domin cimma burin da aka sa gaba.

Abubuwan da suka fi jan hankali a taron sun haɗa da ƙaddamar da makarantar firamare ta Wangara, cibiyar kiwon lafiya ta Gofaro a Gezawa, kaddamar da na’urar samar da iskar oxygen ta farko da ke amfani da hasken rana a asibitin Muhammadu Buhari Specialist Hospital, Nassarawa LGA, da kuma ziyarar ban girma ga Gwamnatin Jihar Kano.

Daga Khadijah Aliyu

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara