Labarai
Kwamishinar Ma’aikatar Mata A Kano Ta Jagoranci Tsaftace Gidan Yara Na Nassarawa
A wani yunƙuri na ƙarfafa muhalli mai tsafta da kare yara daga kamuwa da cututtuka, Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata ta Musamman ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi Sani, ta jagoranci aikin tsaftace Gidan Renon Yara na Nassarawa.
Kwamishinar tare da ma’aikatan ma’aikatar da kuma yaran gidan sun gudanar da aikin tsaftacewar, wanda ya shafi kowanne sashi na wurin.
Ta jaddada cewa wannan shiri wani ɓangare ne na jajircewar ma’aikatar wajen inganta walwala da jin daɗin yara da gwamnati take kulawa da su.

Hajiya Amina ta bayyana cewa daga yanzu aikin tsaftacewar zai kasance na yau da kullum domin tabbatar da tsafta da kuma kare yaduwar cututtuka.
A yayin ziyarar, kwamishinar ta kuma duba shagunan ma’aikatar da ke jikin ggidan, wadanda aka bayar haya.
Sai dai ta nuna damuwa kan ginin da wasu masu haya suka yi ba tare da izini ba, inda suka mamaye filin gidan.
A cewarta, waɗannan gine-ginen suna hana samun damar shiga cikin harabar ginin yadda ya kamata tare da kawo barazanar tsaro ga yaran.

Nan take ta gayyaci Hukumar Tsara Birane da Raya Karkara ta Kano (KANUPDA) domin ta binciki yadda aka mamaye filin su kuma ɗauki matakin da ya dace.
Kwamishinar ta gargadi masu hayar da su guji cin amanar gwamnati, tana mai jan kunne cewa irin wannan “ɗabi’a marar kyau” ba za a lamunce ta ba. Ta kuma tabbatar da aniyar ma’aikatar wajen kare jin daɗin yara tare da ɗaukar mataki kan masu laifi.
“Ma’aikatar za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da muhalli mai tsafta da tsaro ga yara tare da tabbatar da dukiyar gwamnati na cikin kariya,” In ji ta.
Daga Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
