Labarai
Harin Ta’addanci: Gwamnatin Katsina Bukacin Hadin Kan Al’ummar Jihar
Gwamnatin Jihar Katsina ta yi kira ga al’ummomin da ke zaune a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro da su ba da haɗin kai ga jami’an tsaro a ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’addanci da masu garkuwa da mutane.
Mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Faruk Jobe ne ya yi wannan kira bayan taron gaggawa maga da al’amuran tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Katsina.
Jobe ya bayyana cewa an kira taron ne domin sake tantance tsarin tsaron jihar da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa mai tasiri tsakanin hukumomin tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, da yin sintiri a yankuna da kuma musayar bayanai domin tabbatar da nasarar yaƙi da ‘yan bindiga.
Ya ce bisa ga rahotannin baya-bayan nan daga shugabannin hukumomin tsaro daban-daban, jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙarinsu, amma ba za a iya samun gagarumar nasara ba, ba tare da tallafi da haɗin kai daga al’ummomi ba.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa a fannin kayan aikin soja, Jihar Katsina ce tafi shirye-shirye a shiyyar Arewa maso Yamma, tana da motoci masu sulke 43, kayan sintiri da na yaƙi, tare da jajirtattun jami’an Sojojin Najeriya, Rundunar Sama, ‘Yan sanda, DSS, ‘yan sa-kai, mafarauta da kuma jami’an tsoro na jihar wato Community Watch Corps.
Yayin da yake bayyana harin da aka kai a Unguwar Mantau da ke Karamar Hukumar Malumfashi a matsayin aikin ta’addanci na rashin imani, Jobe ya yi ta’aziyya ga mutanen yankin tare da tabbatar da cewa za a kamo masu laifin kuma a hukunta su bisa doka.
“Ba za mu huta ba sai mun kawar da ta’addancin ‘yan bindiga daga jihar nan, sai dai muna bukatar haɗin kai sosai daga al’umma musamman a fannin bayar da bayanai. Dakarunmu ba za su iya aiki su kaɗai ba, suna buƙatar haɗin kai daga al’ummomi.”
Daga Isma’il Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
