Labarai
Isra’ila Ta Ce Za Ta Lalata Birnin Gaza Idan Hamas Ba Ta Amincewa Da Sharuddanta Ba
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa za a lalata birnin Gaza gaba ɗaya idan kungiyar Hamas ta ƙi miƙa makamai da kuma sakin dukkan fursunonin da take riƙe da su.
Wannan furuci nasa ya zo ne bayan majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shirin kai farmaki a birnin Gaza duk da suka da adawa daga ƙasashen duniya da ma cikin gida.
A cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na X, Katz ya ce: “Idan har Hamas ba ta amince da sharuɗɗan Isra’ila na kawo ƙarshen yaƙi a Gaza ba, musamman sakin dukkan fursunoni Isra’ila da kuma miƙa makamai ba, toh babban birnin Gaza zai zama kamar birnin Rafah da Beit Hanoun,” in ji shi.
Wadannan garuruwa biyu da ya ambato dai sun ruguje sakamakon hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a baya.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
