Connect with us

Kasuwanci

Kamfanin Sarrafa Makamai Na Kasa Yasha Alwashin Tamakawa Wajen Dashen Itatuwa

Published

on

Darakta-Janar na Hukumar Kula da Masana’antu na Tsaro ta Najeriya-DICON, Manjo Janar Babatunde Alaya ya ba da shawarar a yi kokarin hadin gwiwa wajen inganta muhalli mai tsafta don jin dadin rayuwar al’umma baki daya.

 

Ya yi wannan kiran ne a wani taron dashen itatuwa da kungiyar Chemical Society of Nigeria-CSN ta shirya, wanda aka gudanar a masana’antar DICON ordnance da ke Kakuri a jihar Kaduna.

 

Manjo Janar Babatunde Alaya ya bayyana cewa dashen itatuwa yana da matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam, domin yana tsarkake iskar da muke shaka.

 

Ya yi nuni da cewa, nan da wasu shekaru masu zuwa, tsiron zai zama inuwa ga mutane da dabbobi, wanda a karshe zai tabbatar da zaman lafiyar al’umma baki daya.

 

Manjo Janar Alaya, wanda ya bayyana shirin DICON na tallafawa wajen fadakar da jama’a muhimancin dashen itace, ya bayyana shirin a matsayin wanda ya dace.

 

Ya kuma yaba wa CSN bisa zabar DICON a matakin farko na gudnaarda wannan aikin.

 

Tun da farko a nata jawabin, shugabar hukumar ta CSN ta jihar Kaduna, Emi-Johnson Umoeka ta bayyana cewa an yi tunanin gudanar da wannan gangamin ne domin yin tasiri ga al’umma ta hanyar shuga bishiyu domin magance saran gandun daji, da kuma yaki da gurbacewar iska, kasa da ruwa.

 

Ta bayyana cewa kungiyar na hada kai da Gwamnatin Jiha tare da zabo Makarantun da za su dasa itatuwa da dama da suka hada da hanyoyin mota.

 

Babban abin da ya fi daukar hankali a taron shi ne babban daraktan hukumar da daraktocin DICON da kuma mambobin CSN na dashen itatuwan.

 

Usman Sani.

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara