Labarai
Shugabar Ma’aikata Ta Kaduna Ta Ja Kunnen Ma’aikata: Ku Rike Da’a, Ku Zama Aminan Jama’a
Shugabar Ma’aikata ta Jihar Kaduna, Jummai Bako, ta bukaci ma’aikatan gwamnati da su hada kai wajen gina al’adar aiki mai cike da gaskiya da rikon amana da kuma da’a.
Ta bayyana hakan ne a wani taron wayar da kai na yini guda a Kaduna, wanda ya kunshi Daraktocin Gudanarwa da Kudi da sauran ma’aikatan gwamnati, mai taken “Ka’idojin Aiki da Ladabtarwa a Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kaduna.”
A jawabinta na bude taron, Jummai Bako ta ce taron ya zama dole sakamakon karuwar rashin da’a a tsakanin ma’aikata, wanda ya jawo wasu lokuta gwamnati ke faduwa a shari’o’in kotu saboda rashin bin tsarin ladabtarwa.
“Mun sha ganin lokuta da dama inda gwamnati ta kai kara kotu amma ta sha kaye, saboda Ma’aikatun da abin ya shafa ba su bi ka’idojin ladabtarwa ba. Wannan shi ne dalilin da yasa muka kira wannan taro domin tunatar da shugabanni kan aikinsu da kuma ka’idojin aiki,” in ji ta.
Ta kara da cewa ma’aikatan gwamnati su ne ginshikin tafiyar da gwamnati, don haka wajibi ne su rike da’a da bin ka’idoji domin inganta amincewar jama’a da hidimar gwamnati.
A nasa jawabin, Daraktan Ofishin Shugaban Ma’aikata, Alexander Garba, ya ce taron ya zo a kan lokaci domin tunatar da Daraktocin Ma’aikatu kan muhimmancin jagoranci na gari da sanin dokoki da gaskiya da sadaukarwa a aikinsu.
Wasu daga cikin mahalarta taron, ciki har da Rakiya Umar da Habiba Mohammed da Yahaya Dauda da Hauwa Tukur da Seth Ali, sun bayyana cewa taron ya kara musu ilimi tare da tunatar da su abubuwan da suka manta, sannan sun yi alkawarin yin aiki bisa ka’ida da horar da ma’aikatansu don inganta ayyuka.

Daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a taron akwai gabatarwar takardu, tattaunawa, da zaman amsa tambayoyi.
VOC: Naomi Anzaku
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
