Labarai
Tattalin Arzikin Najeriya Na Da Karfi Samar Da Karin Jihohi. Inji Dan Majalisa.
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Katagun ta tarayya a jihar Bauchi Alh. Awwalu Abdu Gwalabe, ya bayar da hujjar cewa tattalin arzikin Najeriya na da karfin da zai iya dorewar karin jihohi 12.
Ya bayyana haka ne ga manema labarai a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999 a Arewa maso Gabas a Gombe
Alh. Awwalu Gwalabe, ya ci gaba da cewa, idan har Gwamnatin Tarayya za ta iya kashe Naira tiriliyan 17 wajen gina titin lagos-calabar kadai, hakan na nuni da cewa tattalin arzikin zai iya dorewar samar da karin jihohi.
Ya ce sama da shekaru arba’in ne al’ummar shiyyar katagun a jihar Bauchi suke ta tada jijiyoyin wuya na ganin an samar da jiha amma tsarin mulki da sauran cikas ya hana su yunkurin cimma burinsu.
Dan majalisar ya yi watsi da ikirarin cewa da wuya a samar da karin jihohi a tsarin dimokuradiyya saboda matsalolin da kundin tsarin mulkin kasar ya tanada a cikin tsarin ya ce kawai yana bukatar a sauya wani sashe na Kundin Tsarin Mulki domin a samu sauki.
A cewarsa idan aka gyara bangaren kundin tsarin mulkin kasar da ya amince da kasancewar jihohi 36 da FCT za a iya gyara wanda zai samar da wata hanya ta samar da karin jihohi.
Alh. Awwal Gwalabe ya roki al’ummar shiyyar Katagun da ke jihar Bauchi da kada su karaya, su ci gaba da tara wakilansu a zauren majalisar dokokin kasar domin jihar Katagun ta tabbata.
HUDU/Gombe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
