Labarai
Zamu Yi Aiki Tukuru Wajen Inganta Lafiyar Al’ummar Nijeriya – Lifidin Jama’a
Magatakadan Hukumar kula da lafiya Kofofin Jamata Najeriya CHPRBN Dr. Bashir Idiris Lifidin Jama’a ya bayyana aniyarsa ta inganta ayyukan ma’aikatan hukumar domin samar da ingantaccen kiwon lafiya a Najeriya.
Dakta Bashir Idiris ya bayyana haka ne a Abuja yayin wani taron murnar sake nada shi da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi.
Ya ce hukumar na hada kai da gwamnatin tarayya wajen samar da duk wani kayan aiki don inganta tsarin kiwon lafiya a kasar nan.
Dokta Bashir Idiris ya kuma bayyana cewa daya daga cikin kalubalen da ke gaban fannin kiwon lafiya shi ne karancin ma’aikata sakamakon yadda ma’aikatan ki zurarewa zuwa kasashen waje don neman aiki mai gwabi. inda ya ce gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsare-tsare na tabbatar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikatan lafiya a fadin kasar nan.
Don haka magatakardar ya yi kira ga ma’aikatan lafiya na al’umma da su ci gaba da yin aiki bisa ka’idojin sana’arsu domin ci gaban kasa.
Maryam Idris
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
