Connect with us

Kasuwanci

CORET Tace Mayarda Hankali Kan Samarda Madara Zai Bunkasa Tattalin Arziki Kasan Nan

Published

on

 

Kungiyar Hadin Kan Masu Kiwon Gargajiya ta Afrika (CORET) ta ce mayar da hankali kan samar da madara kaɗai na iya taimakawa matuƙa wajen bunƙasa tattalin arzikin kasan nan.

 

Jami’in Hulɗa da Jama’a na CORET, Aminu Sa’ad, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ilimi da suka kai gonar Arla-Dano da ke Damau, a ƙaramar hukumar Kubau ta Jihar Kaduna.

 

Ziyarar ta zo ne a yayin da kamfanin ya fara bude kofa ga masu ruwa da tsaki domin kara dangantaka da musayar ilimi kan hanyoyin kiwon shanu da samar da madara yadda ya kamata tare da kare muhalli.

 

Gonar, wacce aka zuba jarin sama da dala biliyan goma a cikinta, an kafa ta ne domin nuna mafi kyawun hanyoyin kula da lafiyar dabbobi da tsaftar madara, da kuma kiwo cikin hanyar da ba ta cutar da muhalli.

 

A halin yanzu, gonar na samar da sama da tan 1.5 na madara a kullum, kuma ana ci gaba da faɗaɗa adadin shanun da ake kiwo da kuma samar da abincin dabbobi domin biyan buƙatar kasuwa da ke ƙaruwa.

 

Jami’in Hulda da Jama’a na CORET, Aminu Sa’ad, wanda ya jagoranci tawagar da ta haɗa da kungiyoyin makiyaya daga Ladduga da Damau da Lumu Kwasam, ya bayyana cewa an shirya wannan ziyara ne domin musayar ilimi ga makiyaya.

 

“Muna ƙoƙarin bayyana wa mambobinmu dabarun kiwo mafi inganci da kula da lafiyar dabbobi da tsaftar madara da kuma kiwon da ke kare muhalli – domin su koma su aiwatar a cikin al’ummominsu,” inji shi.

 

Ya ƙara da cewa samar da madara na da matuƙar daraja ga tattalin arzikin ƙasa, kuma yana buƙatar kulawa daga gwamnati.

 

“CORET za ta ci gaba da tallafa wa irin waɗannan shirye-shirye, muddin za su inganta samar da madara daga makiyaya a Najeriya,” inji shi.

 

Shi ma a nasa jawabin, wakilin Hukumar Koyar da Makiyaya ta Ƙasa, Abubakar Lawal Boro, ya yaba da ƙoƙarin CORET da shirin Milk Value Chain wajen tallafa wa ƙungiyoyin makiyaya, musamman a jihohin Kaduna da Jigawa.

 

Ya ce kafa gonar Arla-Dano a Kaduna zai ƙarfafa ƙungiyoyin makiyaya na yankin wajen ƙarfafa haɗakar samar da madara.

 

Shugaban Ayyuka na Arla Foods, Dr. Snori, a nasa jawabin, ya bayyana ranar a matsayin “rana ta musamman da aka ware domin raba ilimi da nuna ƙwazo wajen kiwon dabbobi da samar da madara mai ɗorewa.”

 

Dr. Snori ya nuna albarkatun da Allah ya hore wa Najeriya, inda ya ce: “Muna da fili, rana, da ruwa – Najeriya ya kamata ta zama ƙasa mai fitar da kayan gona zuwa ƙasashen waje.”

 

Ya bayyana cewa gonar Arla-Dano da ke Damau ita ce mafi girma a Najeriya, kuma manufarta ita ce ta bai wa masu ruwa da tsaki kwarin guiwa da kuma ƙarfafa su.

 

“Ta hanyar buɗe ƙofofinmu, muna fatan tayar da sabbin tunani, gina alaƙa, da kuma bayar da gudunmawa wajen inganta sashen samar da madara da kiwo mai ɗorewa a Najeriya,” inji shi.

 

Yayin da yake ƙarfafa mahalarta su shiga cikin al’amura, ya ƙare da cewa: “Ko kai ɗalibi ne, kwararre, ko mai sha’awa kawai, rawar da za ka taka a yau na da matuƙar muhimmanci wajen gina makomar samar da madara a Najeriya.

 

COV: Adamu Yusuf

Labarai

Labarai24 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara