Labarai
Alhazan Jigawa Sun Kai Ziyara Muhimman Wurare A Madina
A wani bangare na kokarin kara ilimantar da mahajjata yayin aikin Hajji, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta fara jagorantar ziyara zuwa wasu wuraren tarihi a Madina.
Yayin jawabi ga mahajjata a Dutsen Uhud, daya daga cikin wuraren da aka ziyarta, shugaban tawagar, Dr Abdulkadir Saleh Kazaure, ya bayyana cewa ziyarar wani muhimmin abu ne ga dukkan mahajjata.
Ya kara da cewa ziyarar za ta karfafa imaninsu kuma ta sa su kara imani da abin da suke karantawa a cikin Alƙur’ani Mai Girma, haka kuma za ta farfado da labarai da tarihin rayuwar Annabi Muhammad (SAW) da sahabbansa, kamar yadda aka bayyana a Suratu Ali Imran, aya ta 97.
Dr Abdulkadir Saleh Kazaure ya bayyana irin kokarin da Annabi Muhammad (SAW) ya yi domin tabbatar da cewa addinin Musulunci, wanda addini ne na zaman lafiya, ya cimma manufofinsa.

Ya bukaci mahajjatan da su yada addinin a kyakkyawan yanayi kuma su kwaikwayi halayen Manzon Allah (SAW).
Ya gargade su da su bi dokoki da ka’idojin da jami’ai suka shimfida don kada su kauce hanya.

Sheikh Dr Kazaure ya kuma bukaci mahajjatan da su amfana da wannan dama ta kasa mai tsarki domin yin addu’o’i da gaske ga kananan hukumominsu, jiharsu da Najeriya baki daya.
Wasu daga cikin mahajjatan da suka zanta da Radio Nigeria sun yaba da yadda jami’an jihar Jigawa suka jagorance su zuwa wuraren tarihi, suna mai alkawarin ci gaba da bin umarnin jami’an yayin da suke a kasar Saudiyya.

Wakilinmu ya kara da cewa, daga cikin wuraren da aka ziyarta akwai Dutsen Uhud, Masallacin Quba wanda shi ne masallaci na farko da Annabi Muhammad (SAW) ya gina, kabarin Sayyidina Hamza da shahidan Uhud, da sauransu.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
