Connect with us

Fasaha

Za a Iya kwashe Mako 5 Ba a Gama Shawo Kan katsewar Intanet a Ghana Ba

Published

on

Za a iya kwashe mako biyar ba a kammala gyara wayoyin da suka lalace na cikin ruwa ba waɗanda suka sa ake samun katsewar intanet a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka, a cewar hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa ta Ghana a ranar Asabar.

Lalacewar wayoyin ta sa an samu gagarumar katsewar intanet lamarin da ya shafi harkokin kasuwanci, da suka haɗa da bankuna da kamfanonin sadarwa da na hada-hadar kuɗi da ma kasuwannin hannayen-jari.

Hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa na Ghana ta ce ta gana da kamfanoni huɗu da ke aikin gyara wayoyin da ke ƙarƙashin ruwa – Africa Coast to Europe (ACE), MainOne, mallakin Equinix, South Atlantic 3 (SAT-3) da kuma the West Africa Cable System (WACS) – da kuma kamfanonin sadarwa.

Ta ce kamfanonin sun gaya mata ainihin wurin da wayoyin suka lalace kuma sun shirya tura ma’aikata domin gudanar da gyaran.

“Kamfanonin da ke gyaran wayoyin sun shaida mana cewa za su kwashe aƙalla mako biyar suna aiki kafin komai ya koma yadda yake,” in ji hukumar.

Ranar Juma’a kamfanin MainOne ya ce ƙwarya-ƙwaryar binciken da suka yi ya nuna cewa wayoyin sun katse ne sakamakon wani motsi da ƙasa ta yi a cikin ruwa lamarin da ya shafe su.

Reuters
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai17 mins ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai48 mins ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci1 day ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha1 day ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha1 day ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai1 day ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi4 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai6 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara