Labarai
Yoro Da De Light Da Heaven Ba Su Yi Atisaye A Man United Ba
Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe.
Ranar Juma’a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za ta kara ranar Laraba a birnin Bilbao.
Yoro ya ji rauni ranar Lahadi a wasan da West Ham ta doke United 2-0, shi kuwa De Light a wasan Brentford ya ji rauni.
Shi kuwa Heaven ya yi atisaye shi kaɗai, sai dai Jonny Evans da Toby Collyer sun yi atisaye tare da ƴan wasan United.
Diogo Dalot ya motsa jiki shi kaɗai, wanda ke fatan buga wasan karshen, amma dai Lisandro Martinez da Joshua Zirkzee sun gama buga wasannin kakar nan, sakamkon jinya.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
