Fasaha
An Nada Shugaban Hukumar Fasahar Sadarwa Da Inganta Tattalin Arziki Ta Jihar Jigawa
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse.
Kafin nadin nasa, Dr. Muhammad Hassan shi ne shugaban hukumar Fasahar Sadarwa da Kimiyya ta Jigawa, wato Galaxy ITT.
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa sabo shugaban hukumar ya sami digirinsa na farko a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero, Kano, a shekarar 2008. Daga bisani, ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Afirka (AUST), Abuja, a shekarar 2011, sannan ya ci gaba da karatu har ya samu digirin digirgir (Ph.D) a fannin Kimiyyar Kwamfuta da Injiniyanci daga Jami’ar Aizu da ke kasar Japan, a 2018.
Haka nan, Gwamnan ya amince da naɗin Baffajo Beita a matsayin sabon shugaban Galaxy ITT.
Kafin naɗinsa, Beita Babban Jami’in Bayanan Fasaha ne a Galaxy Backbone da ke Abuja. Yana da ƙwarewa mai zurfi a fannin fasahar sadarwa, musamman a tsarin gudanar da cibiyoyin sadarwa, tsaro na yanar gizo, da ƙirƙirar fasahar yanar gizo.
Beita ya kammala digirinsa na farko a fannin Kwamfuta daga Jami’ar Anglia Ruskin, kuma ya fara aikinsa ne a Makarantar Informatics ta Jihar Jigawa da ke Kazaure, kafin ya taka muhimmiyar rawa a manyan ayyukan fasahar sadarwa a Turai, Gabas ta Tsakiya, da Afirka (EMEA) a fannoni daban-daban, ciki har da masana’antar mai da gas, da sarrafa kayayyaki, da harkokin kuɗi”.
Bugu da ƙari, Gwamnan ya amince da naɗin Muhammad Nura Zubairu a matsayin Daraktan Zartarwa na Ayyukan Fasaha, da Umar Ibrahim Gumel a matsayin Daraktan Zartarwa na Harkokin Kasuwanci a Galaxy ITT.
Kafin wannan matsayi, Muhammad Nura ya kasance Injiniyan Tallafin Sadarwa a Galaxy ITT, kuma ya kammala babbar difloma (HND) a fannin Tattalin Arzikin Hadin Gwiwa da Gudanarwa daga Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano a shekarar 2010.
“Wadannan muhimman nade-nade na cikin shirye-shiryen Gwamna Namadi na ƙarfafa tattalin arzikin Jihar Jigawa ta fasahar zamani, domin tabbatar da cewa hukumar na da kwararrun shugabanni da za su jagoranci kirkire-kirkire da inganta ayyukan fasahar sadarwa a ciki da wajen jihar” in ji SSG.
Malam Bala Ibrahim ya ƙara da cewa an zaɓi waɗanda aka naɗa ne bisa cancanta, ƙwarewa, da nagarta.
Ya bukaci dukkan waɗanda aka naɗa da su yi aiki tukuru don aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati bisa kyakkyawan.
Sanarwar ta ƙara da cewa, dukkan waɗannan nade-naden sun fara aiki ne nan take.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
