Labarai
Wata Kungiya Mai Zaman Kanta Ta Samar Da Rijiyoyin Burtsatse A Karamar Hukumar Ringim
Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki.
A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu na yin tasiri a rayuwar al’ummar yankin.
A cewarta, wannan aikin yana tabbatar da kudirin gidauniyar na tabbatar da cewa kowace al’umma tana da damar samun tsaftataccen ruwa, ba tare da la’akari da matsayinta ko inda take ba.
Suzie Agas ta jaddada cewa ruwa yana da matukar muhimmanci ga kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki, amma abin takaici, al’ummomi da dama na fuskantar kalubale wajen samun tsaftataccen ruwa.

Ta kara da cewa rashin ruwa mai tsafta yana haddasa cututtukan da ake dauka ta ruwa, yana hana mutane yin ayyuka da kyau, kuma yana rage damarmakin yaran makaranta don mayar da hankali kan karatunsu.
Suzie ta gode wa hukumomin karamar hukumar Ringim bisa goyon baya da hadin kai da suka bayar wajen tabbatar da tsaro da aminci a lokacin aikin.

Ta kuma roki al’ummomin Facawa da Riniyal da su kula da rijiyoyin, don gujewa samun matsala.
A nasa jawabin yayin kaddamar da rijiyoyin, hakimin Sankara, Alhaji Yusi Ahmed, ya tabbatar da cewa wadannan al’ummomi sun shafe shekaru da dama suna fama da karancin ruwa.

Ya ce ko da yake an taba samar da rijiyoyi a wadannan yankuna, rashin kulawa da su ya sa suka lalace.
Ya bukaci mazauna yankin da su dauki nauyin kula da rijiyoyin domin su dade suna amfani da su fiye da wadanda aka samar a baya.
Shi ma da yake nasa jawabi, Shugaban Karamar Hukumar Ringim, Alhaji Badamasi Dabi, ya jinjinawa gidauniyar bisa jajircewarta wajen tabbatar da kammala aikin.

Ya bayyana cewa karamar hukumar Ringim tana da cikakken shirin yin hadin gwiwa da kungiyoyin agaji domin ci gaban al’umma.
Bayan haka, gidauniyar ta rabawa al’ummar buhunan shinkafa.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana godiyarsu bisa wannan aikin, inda suka ce hakan ya rage wahalar da ‘ya’yansu ke fuskanta wajen yin doguwar tafiya domin samo ruwa.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

