Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan Jihar Rivers Da ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar

Published

on

Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida.

A wani jawabi da ya yi  ga alummar kasa ta kafafen yada labarai a ranar Talata, Shugaban kasan ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne sakamakon rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa  a jihar, ya kuma hana gudanar da gwamnati yadda ya kamata kuma ya tauye wa jama’ar Jihar Rivers morar romon  dimokuradiyya.

Shugaban kasan ya nuna damuwarsa kan “mummunan hali” da jihar ke ciki, wanda ya kara muni bayan rushewar ginin Majalisar Dokokin Jihar da gwamnan ya yi a ranar 13 ga watan Disambar 2023. A cewarsa, duk da kokarin da ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka yi don samun sulhu, rikicin ya ci gaba da tsananta.

Da yake magana kan hukuncin Kotun Koli na ranar 28 ga Fabrairu, 2025, wanda ya zargi gwamnan da aikata ayyukan da suka saɓa wa kundin tsarin mulki da raina doka, Shugaban kasa ya ce, “Babu gwamnati a Jihar Rivers, domin bangaren zartarwa ya rushe majalisar dokoki kuma yana mulki tamkar  mulkin danniya.”

Shugaban kasan ya kuma bayyana cewa ya samu rahotannin tsaro da ke nuna barazana ga kadarorin kasa, ciki har da lalata bututun mai da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu biyayya  ga gwamnan ne suka aikata, ba tare da daukar wani mataki  don dakile su ba.

Shugaban kasan ya nada tsohon Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (Rtd), a matsayin mai kula da harkokin Jihar Rivers. Ya bayyana cewa bangaren shari’a na jihar zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba, sannan sabon mai kula da jihar zai kasance yana tsara dokoki ne kawai da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Shugaban kasan ya nuna fatan cewa wannan mataki zai tilasta dukkan bangarorin da abin ya shafa a Jihar Rivers su bi dokokin mulki tare da dawo da zaman lafiya.

Bello Wakili

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara