Ilimi
Yara Mata Sama Da 74,000 Sun Amfana Da Shirin Tallafin Kudi Na AGILE A Kano
Yara mata kimanin 74,452 ne suka amfana da tallafin kudi karkashin shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) a kananan hukumomi 19 na jihar Kano, wanda ya kunshi rukuni na farko da na biyu.
AGILE wani shiri ne na Bankin Duniya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wanda aka kirkira don inganta damar samun ilimin sakandare ga yara mata masu shekaru tsakanin 10 zuwa 20.
Shirin yana daukar matakai da dama domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga yara mata, ciki har da gina da gyara makarantu, da bayar da tallafin kudi ga iyalai masu karamin karfi, da yakar al’adu da ke hana ‘yan mata zuwa makaranta, da karfafa yara mata fasahar zamani, da kasuwanci, da kuma dabarun rayuwa.
a ziyarar da tawagar Kano AGILE (Component 2.1) ta kai zuwa wasu makarantun sakandare a karamar hukumar Makoda, wato GGSS Maitsid, da GGSS Koguna da GGSS Sabon Ruwa, wadanda suka amfana da shirin, sun bayyana cewa tallafin kudi na AGILE ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa iliminsu.
Daliban sun ce sun yi amfani da kudin ne wajen koyon sana’o’in hannu kamar su siyar da kayan kamshi da alewa, da kuma sayen kaya na makaranta kamar uniform, da takalma, da littattafai, da jakunkunan makaranta.
Sun godewa shirin bisa irin tallafin da suka samu.
A nata jawabin, Mataimakiyar Shugaban Tawagar Component 2.1, Hajiya Abu Umar Muhammad, ta bayyana cewa sun kai ziyara Koguna a Makoda domin gano matsalolin da ‘yan mata ke fuskanta wajen karbar kudin tallafi.
Ta ce wasu suna fuskantar matsala da katin ATM, wasu suna samun matsala da sunayensu, da dai sauran matsaloli.
Ta kara da cewa an shigar da ‘yan mata 74,452 a rukuni na farko da na biyu, yayin da 39,000 suka shiga mataki na uku na shirin.
Shugaban karamar hukumar Makoda, Alhaji Auwal Isah Jibga, ya jaddada cewa shirin ya taimaka sosai wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin karamar hukumar da jihar baki daya.
Ya bukaci a ci gaba da shirin kuma ya shawarci dalibai da su yi amfani da kudin ta hanya mafi dacewa da yadda aka tsara.
Wakiliyar Radio Nigeria ta bayyana cewa kafin hakan, tawagar AGILE Component 2.1 ta kai ziyara karamar hukumar Bebeji, inda suka tattauna da dalibai, da malamai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar shirin.
Daga Khadija Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
