Connect with us

Labarai

Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Rukuni Na Farko Na Masu Tsaron Makarantu

Published

on

Gwamna Malam Umar Namadi ya kaddamar da rukuni na farko na jami’an tsaro karkashin shirin Safe Schools Initiative na Jihar Jigawa.

Taron, wanda kuma ya kasance  bikin kammala horo ga masu tsaron, an gudanar da shi ne a sansanin horas da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) da ke Panisau, a Dutse.

Wannan shiri, wanda shi ne irin sa na farko a ƙasar, an kirkireshi ne domin kare makarantu, da asibitoci, da  kotuna, da wuraren samar da ruwa a fadin jihar, inda aka dauki ma’aikata 9,974 don aiwatar da wannan aiki.

Za a tura Jami’an tsaron ne karkashin kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda uku da aka rarraba zuwa mazabun yan majalisun dattawa.

Kamfanonin tsaron sun hada da Kare-Kallo a Jigawa ta Tsakiya, sai  JIMAD a Jigawa ta Arewa maso Yamma, da Corporate Security a  Jigawa ta Arewa maso Gabas.

Wadanda aka dauka sun fito daga sassan jihar daban-daban na jihar, kuma sun hada da masu shaidar karatu ta digiri, da NCE, da difloma, kuma za su yi aiki ne a yankunansu.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kare kayayyakin more rayuwa da tabbatar da dorewar su.

Wannan shiri an kirkireshi ne domin kare jarin da aka zuba a wadannan gine-gine na jama’a. Mun sha ganin yadda barayi ke lalata wadannan gine-gine, suna satar tagogi, kujeru, da sauran kayayyaki masu muhimmanci. A matsayina na shugaba mai kishin al’umma, mun dauki matakan dakile wannan matsala,” in ji shi.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa wannan shiri ba wai tsaro kadai yake bayarwa ba, har da samar da ayyukan yi.

Baya ga kare kadarorin gwamnati, wannan shiri kuma wata dama ce ta samar da aikin yi ga matasa. Kowane daya daga cikin mutum 9,974 da aka dauka daga yankunansu zai tabbatar da tsaron gine-ginen da ke yankinsa.”

Ya bukaci al’ummar yankunan da su baiwa jami’an tsaron hadin kai, yana mai cewa:

A hakika, yakamata al’ummomi su rika kula da tsaron wadannan gine-gine da kansu, amma wannan shiri yana samar da tsari mai kyau na tsaro da ya dogara da al’ummar da ke yankunan.”

 

Da yake yi wa sabbin jami’an tsaron jawabi, ya bukace su da su yi aiki da gaskiya da rikon amana, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da shirin inganta jin dadinsu.

Kayan da kuke sawa alamar iko ne don kare al’umma, ba don tsoratar da su ba. Gwamnati ta ware sama da Naira biliyan 3.4 duk shekara domin aiwatar da wannan shiri, abin da ke nuna muhimmancinsa ga jihar.

Ya bukaci kamfanonin tsaro da ke kula da jami’an da su kula da jin dadinsu, kuma ya roki shugabannin kananan hukumomi da su bada hadin kai don tabbatar da nasarar shirin.

Muna da yarjejeniya kan albashi mai kyau da adalci ga jami’an tsaro. Muna bukatar a kula da su yadda ya kamata, a biya su akan lokaci, sannan a basu kulawa da horo da ya dace domin tabbatar da ingancin tsaro.”

Gwamna Namadi ya bayyana shirin a matsayin wani bangare na karfafa matasa.

 

Usman Muhammad Zaria 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara