Labarai
Gwamna Namadi Ya Kai Ziyarar Bazata Cibiyoyin Ciyar Da Abincin Azumi
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya kai ziyarar bazata ga wuraren bayar da abinci na Ramadan a babban birnin jihar domin duba yadda ake aiwatar da shirin ciyarwar.
Wakilinmu ya ruwaito cewa Gwamnan ya ziyarci cibiyoyi a Dundubus, da Karnaya, da Kaci da Limawa, dukkaninsu a kewayen birnin Dutse.

Yayin bincikensa, Malam Umar Namadi ya yaba wa wasu cibiyoyi bisa jajircewarsu da kishin tabbatar da cewa shirin ciyarwar Ramadan yana tafiya yadda ya kamata.
Sai dai kuma, ya nuna matukar rashin jin dadinsa bayan gano wasu matsaloli na rashin iya tafiyar da shirin a wasu wuraren bayar da abincin.
Gwamnan ya jaddada bukatar kiyaye gaskiya, da adalci da tsafta a yayin rarraba abincin, yana mai kira ga masu ruwa da tsaki da su gyara duk wasu kura-kurai nan take.

Namadi ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin tabbatar da cewa dukkan cibiyoyin ciyarwa na Ramadan suna aiki yadda ya dace, tare da girmama mutuncin al’umma.
Ya kuma tabbatar da cewa za a dauki matakan da suka dace domin inganta yadda ake gudanar da shirin da kuma magance duk wasu matsaloli da aka gano.
Gwamnan ya kuma bukaci hukumomin yankuna da shugabannin al’umma da su kara kaimi wajen sa ido domin tabbatar da aiwatar da shirin cikin tsari.
Ya jaddada cewa jin dadin al’umma na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ke ba muhimmanci.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
