Connect with us

Ilimi

Yara Mata Sama Da 74,000 Sun Amfana Da Shirin Tallafin Kudi Na AGILE A Kano

Published

on

Yara mata kimanin 74,452 ne suka amfana da tallafin kudi karkashin shirin Adolescent Girls Initiative for Learning and Empowerment (AGILE) a kananan hukumomi 19 na jihar Kano, wanda ya kunshi rukuni na farko da na biyu.

AGILE wani shiri ne na Bankin Duniya tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wanda aka kirkira don inganta damar samun ilimin sakandare ga yara mata masu shekaru tsakanin 10 zuwa 20.

Shirin yana daukar matakai da dama domin tabbatar da samun ingantaccen ilimi ga yara mata, ciki har da gina da gyara makarantu, da bayar da tallafin kudi ga iyalai masu karamin karfi, da yakar al’adu da ke hana ‘yan mata zuwa makaranta, da karfafa yara mata  fasahar zamani, da kasuwanci, da kuma dabarun rayuwa.

a ziyarar da tawagar Kano AGILE (Component 2.1) ta kai zuwa wasu makarantun sakandare a karamar hukumar Makoda, wato GGSS Maitsid, da GGSS Koguna da GGSS Sabon Ruwa, wadanda suka amfana da shirin, sun bayyana cewa tallafin kudi na AGILE  ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa iliminsu.

Daliban sun ce sun yi amfani da kudin ne wajen koyon sana’o’in hannu kamar su siyar da kayan kamshi da alewa, da kuma sayen kaya na makaranta kamar uniform, da  takalma, da littattafai, da jakunkunan makaranta.

Sun godewa shirin bisa irin tallafin da suka samu.

A nata jawabin, Mataimakiyar Shugaban Tawagar Component 2.1, Hajiya Abu Umar Muhammad, ta bayyana cewa sun kai ziyara Koguna a Makoda domin gano matsalolin da ‘yan mata ke fuskanta wajen karbar kudin tallafi.

Ta ce wasu suna fuskantar matsala da katin ATM, wasu suna samun matsala da sunayensu, da dai sauran matsaloli.

Ta kara da cewa an shigar da ‘yan mata 74,452 a rukuni na farko da na biyu, yayin da 39,000 suka shiga mataki na uku na shirin.

Shugaban karamar hukumar Makoda, Alhaji Auwal Isah Jibga, ya jaddada cewa shirin ya taimaka sosai wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin karamar hukumar da jihar baki daya.

Ya bukaci a ci gaba da shirin kuma ya shawarci dalibai da su yi amfani da kudin ta hanya mafi dacewa da yadda aka tsara.

Wakiliyar Radio Nigeria ta bayyana cewa kafin hakan, tawagar AGILE Component 2.1 ta kai ziyara karamar hukumar Bebeji, inda suka tattauna da dalibai, da malamai da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar shirin.

Daga Khadija Aliyu 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara