Connect with us

Labaran Ketare

‘Yan Ta’adda Sun Sace Kananan Yara Sama Da 70 A Mozambique

Published

on

Kananan yara fiye da 70 ne ake fargabar bacewarsu a yankin Cabo Delgado na Mozambique bayan wasu sabbin hare-haren mayakan jihadi masu biyayya ga kungiyar IS, wanda zuwa yanzu ya tilastawa mutane fiye da dubu 100 barin muhallansu.

Kungiyoyin agaji da suka kunshi Save the children da kuma MSF na ci gaba da kokawa game da yadda hare-haren ‘yan ta’addan na Mozambique ke ci gaba da lakume rayukan kananan yara inda zuwa yanzu suka tilasta kulle makarantu 129 kamar yadda wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ke bayyanawa.

 

Mahukuntan Mozambique sun tabbatar da hare-haren a arewacin Cabo Delgado duk da cewa basu fitar da cikakkun alkaluman kananan yaran ba, amma sun ce adadin wadanda aka raba su da iyayensu tare da tasa keyarsu cikin dazuka ya haura 70.

A cewar mahukuntan a makwannin baya-bayan nan ne hare-haren ‘yan ta’addan ya sake tsananta inda daga karshen watan Janairu zuwa yanzu, suka raba iyalai fiye da dubu 100 da muhallansu, hare-haren da suka faro tun a shekarar 2017.

 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da kashi 60 na wadanda hare-haren ya fi yiwa illa kananan yara ne kuma adadin na harin baya-bayan nan shi ne mafi yawa da ‘yan ta’addan na Mozambique suka taba kwashewa ta fuskar kananan yara.

 

Akwai dai rahotanni masu alaka da cin zarafi baya ga zartas da hukuncin kisa bisa zalinci da ‘yan ta’addan na Mozambique ke yi kan kananan yara ciki har da wadanda suka sata.

 

 

 

 

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara