Kasuwanci
Damuwar IMF akan kalubalen tattalin arzikin Najeriya yaudara ne – Farfesa Yushau Ango
Damuwar IMF akan kalubalen tattalin arzikin Najeriya yaudara ne – Farfesa Yushau AngoWani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango, ya ce damuwar da asusun lamuni na duniya IMF ke yi kan kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a halin yanzu yaudara ce.
Farfesa Yushau Ango ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Kaduna.
Ya kuma jaddada bukatar hukumar ba da lamuni ta duniya IMF ta gabatar da shawarwari masu inganci don magance kalubalen da ke haifar da cire tallafin man fetur, wanda manufofinsa suka yi tasiri.
Masanin harkokin kudi ya bayyana raguwar farashin kayan abinci a matsayin na wucin gadi sai dai idan ba a samar wa manoman kasar nan abubuwan da suka dace da suka hada da taki mai rahusa domin bunkasa noma.
Farfesa Yushau Ango ya kuma yi nuni da cewa, rage farashin man da wasu kamfanonin mai ke yi, ana sa ran zai sa masu ababen hawa za su samu saukin amfani da man.
Ya kuma yi kira da a samar da dorewar manufofin tattalin arziki domin kiyaye ka’idojin mulkin dimokuradiyya.
COV/ SULEIMAN KAURA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
