Kasuwanci
An Bukaci ‘Yan Fansho Su Matsa Kaimi Har Sai Anbiya su Hakokinsu
An Bukaci ‘yan fansho suyi gangami ganin jinkirin da ake samu wajen biyan su kudaden su.
An shawarci kungiyar ’yan fansho ta tarayya da ta zaburar da mambobinta kan jinkirin rage basussukan da gwamnatin tarayya ta amince da su.
Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ’yan fansho na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Alhaji Muhammad Mamman, ya bayar da wannan shawarar a matsayin martani ga rahotannin da ke cewa an dakatar da zanga-zangar da ake shirin yi kan lamarin, biyo bayan rokon da PTAD ta yi na a ba da damar tattaunawa.
Alhaji Muhammad Mamman wanda ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawa da wa’adin makonni hudu da hukumar NIPOST reshen kungiyar ‘yan fansho ta kasa ta bayar ya ba da shawarar fadada taron kungiyoyin domin ganin an warware matsalolin da aka samu wajen biyan basussukan da ake bin su.
Ya ji takaicin yadda duk da alkawuran da hukumar ta yi na biyan kudaden alawus-alawus din, har yanzu wadanda suka yi ritaya ba su samu kudaden da kungiyoyin da abin ya shafa suka amince da su ba.
Alhaji Muhammad Mamman ya jaddada bukatar kungiyoyin su kai kara ga Majalisar Dokoki ta kasa, EFCC da ICPC idan har aka kasa cimma matsayar tattaunawa kan lamarin duba da yadda ake zargin karkatar da kudaden fansho a baya ba tare da isassun hukumcin da zai kawo gyara ga lamarin ba.
COV/ SULEIMAN KAURA
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
