Labarai
Jihar Jigawa Ta Yi Garambawul Ga Dokar Bada Tallafi Ga Masu Bukata Ta Musamman
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma.
Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar.
Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau.
Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran masu bukata ta musamman da ke amfana da wannan tallafi daga mutane 150 zuwa 200 a dukkan kananan hukumomin jihar 27.
Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim ya yi nuni da cewar, karin yawan tallafin da kuma wadanda su ke amfana na daga cikin kudurin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta rayuwar masu rauni a cikin al’umma.
Ya bukaci dukkan masu bukata ta musamman a fadin jihar, su ci gaba da gudanar da addu’oi ga gwamnatin jihar da sauran shugabanni domin samun sukunin sauke nauyin da ke kan su tare da wanzuwar zaman lafiya da cigaban tattalin arziki da zamantakewa a Jigawa da Najeriya ba ki daya.
Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar ya gudanar da karatu na 3 akan kudurin, sai shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin ya zamo doka.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
