Kasuwanci
Gwamnatin Jigawa Za Ta Horas Da Manoman Alkama A Birnin Kudu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi alkawarin horar da matasa da ke aikin noman alkama a karamar hukumar Birnin Kudu.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba gonakin alkama a yankin.

Ya yabawa Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr Muhammad Uba Builder bisa wannan shiri da ya bayyana a matsayin wata hanya ta samar da aikin yi ga matasa da bunkasa harkar noma.
Kazalika, a yayin ziyarar gani da ido, Malam Umar Namadi ya kuma ba da umarnin gaggauta gina katanga da kuma gina ofishin jami’an tsaro a sabuwar tashar bada ruwan sha mai amfani da hasken rana ta garin Birnin Kudu.

Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa, ya shaida wa Gwamnan cewar, an haka rijiyoyi goma sha bakwai a wurin.
A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Uba Builder, ya bayyana cewa Karamar Hukumar ta dauki matasa kimanin 170 don yin noman alkama.
Builder, ya ce daukar matasan na da nasaba da tallafawa kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arzikin al’umma.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
