Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Al’umma Da Su Rika Taimakawa Hukumomin Tsaro Da Muhimman Bayanai

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron  kasar nan.

Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a na gwamnatin jihar Jigawa da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu.

A cewar sa, kiran ya zama wajibi domin karfafa tsaro a fadin Najeriya.

Alhaji Badaru Abubakar, ya yi nuni da cewa an samu ingantuwar harkokin tsaro a fadin kasar cikin ‘yan watannin nan.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi iya bakin kokarinta wajen yaki da rashin tsaro, kuma za ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofin da ake so.

Ministan ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da bayar da duk wani tallafi ga sojojin Najeriya da ke fagen fama don tabbatar da an maido da tsaro.

Badaru Abubakar wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya bayyana jin dadinsa da yadda ya mika ragamar shugabanci ga gwamnati mai inganci.

Ya yabawa gwamnatin Gwamna Umar Namadi bisa gagarumin ayyukan raya kasa da aka gudanar a jihar cikin shekara daya da rabi.

Na yi farin cikin ganin manyan  ayyukan raya kasa da wannan gwamnati ta aiwatar, a cikin shekara daya da rabi da ta wuce,” in ji Ministan.

Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Aminu Usman, da tsohon gwamnan jihar  Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim, da sarakuna da malaman addinai, da manyan jami’an gwamnati da dai sauransu.

 

Usman Muhammad Zaria.

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara